Mr shaaban

in preching •  8 years ago 

ROMO TUN A GIDAN DUNIYA
Wata rana Imamu Ahmad bin hambalI yayi tafiya zuwa wani gari...
Inda ya tsinci kansha CIKAKKEN BAKO..
Duk da cewa sunan shi ya bazu a duniya; sai dai ba kowa ba ne ya sanshi a fuska..
Saboda a wancan lokacin babu hoto..
Saboda haka ya sauka a wani masallaci...
Da dare yayi mutane suka watse, sai wani daga cikin masu gadin masallacin ya nemi ya fitar dashi..
Saboda dokar su ta hana kwana a masallaci...Sai Imam Ahmad ya fito ya zauna bakin kofa...Mai gadin nan ya Kara biyo shi yace lallai sai ya tashi...
Da yaga imam ahmad zai bata mashi Lokaci, sai ya kama kafarshi ya jawo shi har bakin hanya...
Dadai wurin da ya ajiye shi Akwai shagon wani dattijo yana gasa gurasa...
Sai ya tausaya ma wannan bakon, ya bashi wuri a shagon shi ya kwana...
Shi kuma ya cigaba da aikinshi, yana kwaba filawa amma kuma bakin shi yana anbaton Allah:
*SUBHANALLAH
*WALHAMDU LIL LAH
*LAA. ILAHA ILLALLAH
*ALLAHU AKBAR
Haka ya cigaba har gari ya waye..
Imam Ahmad yayi mamaki, sai ya tambaye shi:
Tun yaushe kake wannan azkar?
Tun ina matashi na saba ma baki na da anbaton Allah, sai Allah ya sauqaqa min Shi kamar yadda nake numfashi..
sai Imam Ahmad yace. To wane fa'ida ka samu albarkacin wannan kyakkyawa aiki...
babu abinda zan roki Allah ya hana ni..!
yanzu duk abinda ka roki Allah ya baka!?
kwarai kuwa, sai dai abu guda daya...
sai Imam Ahmad yace menene shi?
sai yace na roki Allah ya nuna min Ahmad bin Hanbal, amma har yanzu ban amsa min ba...ALLAHU AKBAR.........
Da imam Ahmad ya ji haka sai yace:
ALLAHU AKBAR, yau gashi Allah ya kawo ma Ahmad har shagon ka ana janshi a kasa...
Ya Dan Uwa na Ban San wata falala da zaka samu ba idan ka yawaita zikiri kuma ka tura wannan sako ga abokai da yan uwa
Amma dai nasan annabi yace:
Wanda yayi nuni zuwa ga wani aikin alheri, yana da kwatankwacin ladan Allah ya bamu ikon yin aiki da umurni da aikin alkhairi

Authors get paid when people like you upvote their post.
If you enjoyed what you read here, create your account today and start earning FREE STEEM!
Sort Order:  

Hi! I am a robot. I just upvoted you! I found similar content that readers might be interested in:
https://www.sv-se.fr-fr.prod.facebook.com/Rijalus-Sunnah-Taskar-Imam-Mustapha-Ashaka-406956209465038/

Great