Barka dai, ‘yan uwa da abokai. Ranar 20 ga watan

in hive-137029 •  2 years ago 

Barka dai, ‘yan uwa da abokai. Ranar 20 ga watan Afrilu, rana ce ta Guyu bisa kalandar gargajiyar Sin, wato Grain Rain a bakin Turawa. Wannan lokaci na zuwa a karshen lokacin bazara, wanda ya alamta karuwar yawan ruwan sama. A lokacin, mu Sinawa mu kan sha shayi tare da fatan samun lafiyar jiki.
Yau na samu damar tsintar ganyayen shayi da kuma sarrafa su. Wannan ne karo na farko da na gwada wannan aiki, gaskiya akwai wahala sosai. Ina jinjinawa dukkan manoman dake gudanar da wannan aiki.
Allah ya ba mu girbin hatsi da koshin lafiya. Amin.
1688329511186.jpg

1688329507423.jpg

1688329503362.jpg

Authors get paid when people like you upvote their post.
If you enjoyed what you read here, create your account today and start earning FREE STEEM!